Kano Ce Kawai Ke Bin Tsarin Yaki Da Rashawa A Najeriya – Ganduje

Rahotanni daga birnin Kanon Dabo na bayyana cewar Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Alhamis ya bayyana cewa a jihar Kano kadai ake yaki da cin hanci da rashawa kamar yadda gwamnatin tarayya ke yi.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin rantsar da kwamitin tafiyar da dabarun yaki da rashawa na hukumar korafe-korafe da yaki da rashawan jihar Kano.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya ce wannan ne kwamiti mafi muhimmanci da za’a rantsar kan yaki da rashawa.

“A jihar Kano kadai ake yaki da rashawa kamar yadda akeyi a gwamnatin tarayya. Ina mai tuna cewa kwamishanoni biyu da sakatarorin din-din-din sun rasa kujerunsu sakamakon ayyukan hukumar yaki da rashawa,”

Ganduje yace. “Hakan na nufin cewa babu wanda ya fi karfin a hukuntashi idan aka kamashi da kashi a gindi. Hakan na nufin cewa hukumar na aiki. Ko ku yarda, ko kada ku yarda, rashawa na kashe mu.” Ganduje ya jinjinawa ayyukan shugaban hukumar, Muhuyi Rimingado, wajen dakile cin hanci da rashawa.

Labarai Makamanta