Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya yabawa Gwamnatin Tarayya a kan kafa wata katafariyar tashar samar da wutar lantarki a karamar hukumar Bichi domin bunkasa samuwar wutar lantarki a jihar.
Hakan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan sadarwa da hulda da jama’a na gwamnan, Malam Ameen Yassar ya fitar.
Ganduje ya yi wannan yabon ne yayin da yake karbar bakuncin Shugaban Kamfanin rarraba wutar lantarki (TCN), Alhaji Sule AbdulAziz, wanda ya ziyarce fadar gwamnatinsa da ke birnin Kanon Dabo.
Kamar yadda Gidan Talabijin na kasa NTA ya ruwaito, gwamnan ya ce wannan katafaren aiki zai kawo ci gaba da habakar tattalin arziki a jihar bayan gushewar annobar korona.
Ganduje ya yi godiya ga shugaba Muhammadu Buhari da kuma Ministan Lantarki da suka jajirce a kan taimakawa jihar wajen farfado da tattalin arzikinta, musamman ma bayan an gama da kalubalen cutar korona.
You must log in to post a comment.