Kano: Bada Zakka Ya Zama Dole Ga ‘Yan Siyasa

Darakta janar na hukumar Zakkah da Hisbah na jihar Kano, Safiyanu Abubakar, yace ana shirin mayar da biyan Zakka ya zama wajibi ga dukkan ‘yan siyasa kafin su tsaya takara a jihar.

Abubakar ya sanar da hakan a ranar Alhamis a ofishinsa yayin rantsar da kwamitin mutum 11 na karbar Zakka a jihar.Kamar yadda yace, wannan al’amarin ana son tabbatar dashi ne domin taimakon mabukata a jihar.

“Ya zama dole ga kowannen mai hali ko kungiya da su fitar da wani kaso na dukiyarsu a matsayin Zakka,” domin rage raɗadi ga mabuƙata a faɗin Jihar.

Abubakar ya kara da yin bayanin cewa hukumar ta zo da wannan sabon salon ne ta yadda kowanne mai hannu da shuni zai biya zakka.

“Yan majalisun jihar, ballantana na kwamitin lamurran addinin sun zauna tare da tattaunawa a kan muhimmancin Zakka. “A matsayinmu na kwamitin, muna kokarin kaiwa matsaya ta yadda duk mai neman wata kujera a jihar sai ya bada shaidar yana biyan Zakka ga hukumar”.

Labarai Makamanta