Kano: Ba Mu Amince Da Sharuddan Kwamitin Sulhu Ba – Shekarau

Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa APC ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau ta yi watsi da ƙa’idojin sasantawa da sharuɗɗan da kwamitin da uwar jam’iyya ta ƙasa ya gindaya domin kawo ƙarshen ruɗanin shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano.

Ɓangaren na Shekarau ya fitar da wannan sanarwa a ranar Litinin, a matsayin raddi da martani ga kwamitin da Shugaban APC na Riƙo na Ƙasa, Mala Buni ya kafa domin sasanta rikicin Kano.

Kwamitin Sasanta Rikicin APC a Kano, ya ƙunshi Gwamna Bello Matawalle na Zamfara, tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara da kuma Sanata Abba Ali.

Sharuɗɗan Da APCin Shekarau Ta Watsa Bola Sune Kamar Haka:

  1. Cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ne zai kasance jagoran APC a Kano. A matsayin sa na shugaba, ya kasance ya na nuna jagorancin tafiya tare da kowa.
  2. Cewa shari’ar da suke ta kafsawa a kotu ba abin alheri ba ne, domin nan gaba babu ɓangaren da zai iya yin nasara ba tare da haɗin kan ɗaya ɓangaren ba.
  3. Ganduje ya riƙa jan ɓangarorin ko’ina na jam’iyyar APC a jika, domin a gina APC da ɗimbin mabiyan ta a Kano.
  4. Cewa ana jaddada wa ɓangarorin su sani sasantawa ta gaskiya, ita ce wadda aka cimma yarjejeniya ta hanyar yin sulhu. Ma’ana, babu ɓangaren da zai samu yadda ya ke so ɗari bisa ɗari.

Labarai Makamanta