Kano: Ana Bincike Kan Budurwar Da Ta Rataye Kanta

Rundunar ƴan sandan jihar Kano a tana ci gaba da bincike kan abin da ya sa wata budurwa mai shekara 17 ta rataye kanta a ƙauyen Garin Dau da ke yankin karmar hukumar Warawa.

Mafi akasarin mazauna ƙauyen dai sun yi zargin cewar budurwar ta rataye kan nata ne bisa auren dole da iyayenta ke shirin yi mata.

Sai dai iyayen nata sun musanta wannan zargi inda suka ce ba ta kammala makarantar sakandare ba, balle a yi maganar aurar da ita.

Faruwar wannan lamari dai ya ya zowa mazauna yankin da mamakin sakamakon yadda da dama daga cikin mutanen kauyen ke bayyana budurwar da kyawawan ɗabi’u.

A yau ne aka shiga yini na biyu na rasuwar Safiya mai shekaru 17 da ke aji biyu a makarantar sakandare, wadda aka tarar da gawarta a rataye kuma ana zargin ita ta rataye kanta.

Labarai Makamanta