Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Tsohon Gwamnan jihar Sanata Ibrahim Shekarau; Sanata Barau Jibrin da wasu mambobin majalisar wakilan tarayya sun kai ƙara wajen Sifeto Janar na yan sanda, IGP Baba Alkali kan rikicin APC a Jihar.
Yan majalisan sun shigar da kara hedkwatar yan sanda ne bisa harin da aka kai ofishin yakin neman zaben Sanata Barau Jibrin ranar Alhamis, 2 ga Disamba.
Wadanda suka sanya hannu kan takardar sun hada da Sanata Shekarau (Kano ta tsakiya), Sanata Barau (Kano ta kudu), ;Nasiru Abdua, Tijjani Abdulkadir Jobe, Shaaban Sharada, da Haruna Isa Dederi.
‘Yan majalisan sun ce an kai harin ne sakamakon nasarar da suka samu a kotu. Abdullahi Abbas, Sule Garo da wasu yan siyasa 5 suka dau nauyin kaiwa ofishinmu hari.
A karar da suka shigar, sun ce Shugaban jam’iyyar na bangaren gwamna, Alhaji Abdullahi Abbas da kwamishanan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo, suka dau nauyin hare-haren.
Sauran wadanda sukayi zargi sune shugaban karamar hukumar Kano Municipal, Faizu Alfindiki; Shugaban karamar hukumar Gwale, Khalid Ishaq Diso; Shugaban karamar hukumar Kumbotso, Hassan Garban Kauye; da Shugaban karamar hukumar Nasarawa, Auwal Lawan Shuaibu.
Wani sashen karar yace: “Zaku tuna cewa ranar 30 ga Nuwamba, babbar kotun Birnin tarayya ta yanke hukunci kan lamarin zaben shugabannin APC a Kano kuma wadanda suka sha kasa basu ji dadi.” “Maimakon su yi yakinsu a kotu, sun koma kai hare-hare.” “Sun yi kokarin kona ofishin jam’iyyarmu dake Zaria Road don kashe mazauna da ji musu rauni.”
You must log in to post a comment.