Kano: An Wajabta Yin Gwajin Kwakwalwa Ga ‘Yan Siyasa

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin Ganduje tace duk wani mamban jam’iyyar APC dake neman wani mukamin jam’iyya sai ya yi gwajin shan miyagun kwayoyi.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Muhammad Garba, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, kuma aka rarraba ta ga manema labarai a birnin Kano.

Kwamishinan ya shawarci dukkan yan takara da su je ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ranar Talata da misalin ƙarfe 7:00 na safe domin gudanar da bincike a kansu.

Bugu da ƙari, Kwamishina yace sai da aka gudanar da makamancin irin wannan gwajin ga yan takara a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi. Hakanan sai da aka yiwa duk wani mai rike da mukamin siyasa na jiha, da ya haɗa da mambobin kwamitin zartarwa na jihar Kano, kafin a basu ofishinsu.

Garba ya ƙara da cewa tuni gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya sanar da hukumar NDLEA ta gudanar da gwajin. Ya kuma yi gargaɗin cewa gwamnati zata ɗauki mataki kan duk wanda ta gano yana ma’amala da wasu haramtattun kwayoyi kuma ba kan ƙa’ida ba.

Garba yace yayin zaɓen shugabanni a matakin ƙananan hukumomi, aƙalla yan takarar kansila 13 aka dakatar, kuma aka maye su da wasu bayan gwajin NDLEA ya bayyana suna ma’amala da kwayoyi.

“Wannan gwamnatin ta shirya sosai wajen yaƙi da safarar miyagun kwayoyi da kuma amfani da kwaya ba bisa ƙa’ida ba.”

Labarai Makamanta