Kano: An Shiga Rudani Bayan Mutuwar Dalibar Jami’ar Bayero

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Wata daliba dake ajin ƙarshe a tsangayar Ilimi ta jami’ar Bayero dake Kano (BUK), Binta Isa, ta rasu a ɗakin kwanan dalibai ranar Juma’a 26 ga watan Nuwamba, 2021.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’ar ta fitar a shafinta na Facebook ɗauke da sa hannun mataimakin rijistara, Lamara Garba.

Ɗalibar wacce ta fito daga jihar Kogi, ta rasa rayuwarta ne da misalin ƙarfe 7:00 na dare bayan fama da gajeruwar rashin lafiya da ta danganci ciwan ƙirji.

A cewar daraktan lafiya na jami’ar, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, Binta ta je Asibitin jami’a na New Campus a ranar 24 ga watan Nuwamba, inda ta yi korafin tana fama da ciwan ƙirji.

Ya ƙara da cewa jami’an da suka duba mamaciyar a lokacin, sun bata magani tare da zayyana mata yadda zata yi amfani da su. Daraktan ya bayyana cewa daga nan Binta ta samu sauki, domin ta cigaba da halartan Lakca ranar Alhamis da Jumu’a, kuma ta cigaba da ayyukan karatunta.

“A ranar Jumu’a 26 ga watan Nuwamba, 2021 da yamma, lokacin sallar Magriba, ta shaida wa abokiyar zaman ɗakinta cewa tana jin ciwan ƙirji, amma a haka ta kokarta ta yi Alwala domin ta yi sallar Magrib a ɗakin.”

“Abokan zamanta a ɗakin sun kaɗu kuma sun tsorata da suka dawo suka tarad da ita ta yi warwas a ƙasa.” “Nan take suka sanar da mutane, akai gaggawar kaita asibitin koyarwa na Aminu Kano, inda likita ya tabbatar da cewa ta rasu.”

Mataimakin shugaban BUK, Farfesa Sagir Adamu Abbas, tare da rijistara, Jamil Ahmad Salim, daraktan lafiya da darakan tsaro, Abdulyakin Ibrahim duk sun halarci wurin da lamarin ya faru.

A halin yanzun jami’a ta sanar da ɗan uwan ɗalibar, wanda yake zaune a cikin garin Kano, game da lamarin da ya faru BUK ta yi jimamin wannan rashi VC Farfesa Adamu, a madadin jagororin BUK, malamai da ɗalibai, ya bayyana damuwarsa da rasuwar matashiya Binta Isa, wacce ta mutu ta na gab da kammala karatunta.

Ya kuma mika ta’aziyya ga iyayenta, yan uwa da abokan karatu, kuma ya yi addu’a Allah ya yafe mata kura-kuranta, ya sa tana daga cikin yan Aljanna.

Labarai Makamanta