Kano: An Shiga Firgici Sakamakon Ganin Baƙi Masu Raƙuma

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kwantar wa jama’a da hankula game da wasu baƙin mutane tare da rakuma da suka bayyana a sassan Birnin jihar.

Mazauna jihar sun ankarar da ‘yan sanda kan baƙin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar a cikin makon nan.

Wasu mazauna birnin sun zargin matafiyan sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa. Baƙin sun yada zango a Rimin Zakara da Dorayi a karamar hukumar Gwale ta jihar Kano.

Mataimakin Sufurutandan ‘yan Sandan Jihar ASP Haruna ya ce sun yi bincike tare da hukumar kula da shige da fice (Immigration) sun gano cewar baƙin na ɗauke da takardun izinin shigowa kasar.

“Ba mu same su da wani abu mai alaka da laifi ba. Bincike ya nuna dillalan kanwa ne daga Jamhuriyar Nijar kuma suna da takardun shigowa kasar.

“Mun gayyaci shugabanninsu domin tambayoyi, kuma mun tuntubi ofishin jakadancin Nijar kan batun. “Binciken da muka kara yi ya nuna cewa ba za su wuce kwanaki 20 ba idan suka sayar da hajarsu sannan suka sayi kayan abinci a kasuwar Dawanau domin komawa gida Damagaram.

Labarai Makamanta