Kano: An Sanya Ranar Muƙabala Tsakanin AbdulJabbar Da Malamai

Rahotanni daga jihar Kano na bayyana cewar gwamnatin Jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta sanya ranar da za’a fafata muƙabala tsakanin Abduljabbar da Malaman Kano, domin kawo karshen tataburzar dake faruwa a tsakanin su.

Fadar Gwamnatin Jihar Kano da ke ta tabbatar wa da BBC cewa ranar Lahadi, 7 ga watan Maris aka shirya fafata muƙabalar tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai ya ce sun shirya tsaf domin gudanar da muƙabalar.

Shi ma Kwamishinan Harkokin Addini Dr. Muhammad Tahir ya tabbatar da BBC saka ranar.

Tun a ranar 7 ga Fabarairu ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince a gudanar da muƙabalar kuma aka faɗa wa ɓangarorin biyu su shirya fuskantar juna a tattaunawar ilimi.

Gwamnatin Kano ta zargi malam Abduljabbar Nasiru Kabara ne da yin “kalaman tayar da fitina game da addinin Musulunci” bayan wasu malamai a jihar sun zarge shi da saɓa wa abin da Musulunci ya zo da shi.

Labarai Makamanta