Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta janye dokar da ta hana ƴan adaidaita-sahu bin wasu manyan tituna cikin kwaryar Kano.
Shugaban Hukumar kula Da Zirga-zirgar Ababen-hawa, KAROTA, Baffa Babba Dan’agundi ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai a Kano.
Ya ce an janye dokar ne saboda matuƙa baburan adaidaita-sahu ɗin sun yi biyayya kuma al’umma sun yi suka a kan dokar.
You must log in to post a comment.