Kano: An Gaza Samun Matsaya A Rikicin Shugabancin APC

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar an kasa cimma matsaya a sulhun da jam’iyyar APC mai ke ƙoƙarin yi tsakanin ɓangaren gwamna Abdullahi Ganduje da Sanata Shekarau.

Shugaban riƙo na jam’iyyar kuma gwamnan jihar Yobe Maimala Buni ne ya jagoranci wasu gwamnoni wajen ganawa da tsagin jam’iyyar a jihar da ke ƙarƙashin tsohon gwamna, Senata Ibrahim Shekarau da da aka fi sani da G7 da nufin sulhunta tsakaninsu da tsagin Ganduje.

Sun yi zaman ne a Abuja, amma rahotanni na nuna cewa da yiwuwar su ci gaba da ganawar.

Labarai Makamanta