Kano: An Damke Tsohon Kwamishina Sakamakon Zagin Ganduje

‘Yan sanda a Kano sun gabatar wa da lauyoyin Injiniya Mu’azu Magaji tuhume-tuhumen da ake yi masa na cin mutuncin Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.

An kama Injiniya Mu’azu ne a Abuja bayan kammala wata tattaunawa da gidan talabijin na Trust TV.

Barista Garzali Datti Ahmad na ɗaya daga cikin lauyoyin injiniyan kuma ya faɗa wa BBC cewa daga cikin tuhumar akwai ɓata sunan Gwamna Ganduje da zagin sa da cin mutuncin iyalain sa da yunƙurin haddasa tashin hankali.

Baristan ya ƙara da cewa gwamna ne ya kai ƙorafi kan Injiniya Mu’azu, wanda shi ne tsohon kwamashinan ayyuka ƙarƙashin mulkin Gandujen.

Labarai Makamanta