Kano: An Damke Dan Chanan Da Ya Yi Wa Budurwa Yankan Rago

Shaidun gani da ido sun tabbatar da faruwar lamarin wanda bayanai ke cewa ya faru ne da misalin karfe 9 na daren ranar juma’a kamar yadda wani makwabcin gidan da abin ya faru Abubakar Mustpha ke cewa yarinyar da aka bayyana sunanta da Ummita wadda daliba ce a kwalejin horar da Ungozoma da malaman jinya ta jihar Kano, bazawara ce kuma ana ganinsu lokaci zuwa lokaci da dan Chinan.

 

A cewar wasu bayanai yarinyar wadda cikakken sunanta shi ne Ummakulsum Sani Buhari mazauniyar unguwar Janbulo da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, tun gabanin ta yi aure suna tare da dan Chinan mai suna Geng Quangron gabanin iyaye su ki amincewa da batun aurensu dalilin da ya tilasta rabuwarsu.

Sai dai kamar yadda mahaifiyar yarinyar ta shaidawa jaridar daily Trust tun bayan fitowar Ummita daga gidan mijinta, dan Chinan yafara zarya a kofar gidansu amma ba a bashi damar haduwa da ita, saboda ta ki amincewa da soyayyarshi a wannan karon.

Wani makwabcin su Marigayiyar na daban Muhammad Sani ya ce akwai lokacin da dan Chinar ya yi kokarin kashe kansa saboda budurwar tasa amma jami’an tsaro suka shiga tsakani tare da lallaba shi.

Mahaifiyar Ummita da ke bayyana yadda dan Chinar ya kashe ‘yar tata, ta ce dan Chinan yana yawan zuwa gidan da nufin ganin yarinyar amma bata amincewa, sai dai a ranar da abin ya faru ya yi ta sintiri tare da buga kofar gidan har zuwa lokacin da ake tsaka da tsala ruwan sama a daren ranar.

A cewar mahaifiyar bugun da ya ke yiwa kofar gidan da karfin tsiya ne ya sanya ta zuwa bude kofar don yi masa bayani a kokarinta na ganin bai tara musu jama’a a kofar gida ba, amma kuma bude kofar keda wuya sai ya angajeta tare da kutsa kai cikin gidan da wukarsa a hannu tare da daddaba mata tako’ina a jikinta.

Mahaifiyar Ummita ta ci gaba da cewa ko da ta fara ihu tare da neman taimakon mutane, ba a iya jiyo maganarta saboda kakkarfan ruwan saman da ke zuba a lokacin, sai daga baya wasu suka jiyo tare da kutsa kai cikin dakin, amma tun gabanin suje rai ya yi halinsa ko da ya ke anyi gaggawar mika Ummita ga asibiti don tabbatarwa.

Bayanai sun ce al’ummar Unguwa ne suka kamo dan Chinar lokacin da ya fita da gudu a kokarin tserewa tare da mika shi ga jami’an tsaro.

Tuni dai aka yi Jana’izar Ummita da misalin karfe 10 na safiyar yau asabar bisa tanadin koyarwar addinin Islama.

Labarai Makamanta