Kano: An Damƙe Wani Ƙato A Ɗakin Kwanan Ɗalibai Mata


Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar an yi nasarar cafke wani garjejen ƙato a cikin Ɗakin kwanan dalibai Mata na jami’ar Bayero dake Kano, kwance cikin mayafi guda da wata daliba da talatainin dare.

Lamarin ya faru ne a unguwar Danbare da ke kusa da jami’ar Bayero BUK a Kano bayan wani samame da hukumar Hisbah a jihar suka kai a wasu dakunan kwanan daliban jami’ar inda suka kama dalibai mace da namiji a daki guda cikin mayafi guda.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba a Danbare, wata unguwa da ke kallon kofar shiga jami’ar ta Bayero a birnin na Kano.

An gano cewa ‘yan hisban sun afka cikin dakunan daliban sun tafi da su ofishinsu ba tare da ɓata lokaci ba.

Wata majiya ta ce sumamen da ‘yan hisban suka kai ya tada hankulan wasu ‘yan unguwar da suka kasa yin barci saboda tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo.

Hukumar ta Hisbah da aka kafa a wasu jihohin arewa domin tabbatar da bin dokokin addinin musulunci ta hana abubuwa kamar askin banza, sauke wando kasa da kugu, saka kida a wuraren biki da wasu abubuwan da suka saba koyarwar addinin musulunci, sannan uwa uba yaƙi da baɗala ta karuwai.

A kwanakin baya, Hisbah ta aske wa wasu matasa kai sakamakon askin da suka yi na ado sun kuma kama wasu saboda saka wasu tufafi da suka ce ba su dace ba. Sun kuma yi suna wurin kwace giya da lalata su a jihohin da suke aiki.

Labarai Makamanta