Kano: AbdulJabbar Ya Zargi Lauyoyi Da Gaza Ba Shi Kariya

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Rikici ya barke a kotun shari’ar musulunci ta jihar Kano yayin da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda lauyoyinsa basu kare shi a gaban kotu.

A karo na biyu shehin malamin ya zargi lauyoyinsa da rashin kareshi idan ana kawo shaida kuma basu ba shi dama ya kare kanshi. An ruwaito cewa Malam Abduljabbar ya roki kotu ta bashi dama ya kare kansa tunda lauyoyinsa basu iyawa.

Mai sharia Ibrahim Sarki Yola, ya yi watsi da bukatar malamin, inda ya koma kan lauyansa, Umar Mohammed, wanda ransa ya baci bisa abinda wanda yake karewa ya yi.

Gwamnati ta gabatar da shaidu Tun da farko, a zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan gwamnati, Farfesa Mamman Lawan Yusufari (SAN), ya gabatar da shaidarsa ta farko. Lauyan ya gabatar da wani mai suna, Adamu Muhammad, mai sana’ar ɗinki a Gwale, wanda ya tabbatar da cewa shi ɗalibinsa ne mai bibiyar karatunsa.

Adamu ya shaidawa kotu cewa ba ɗaya ba kuma ba biyu ba yaji Sheikh AbdulJabbar yana kalamai marasa daɗi ga Manzon Allah (SAW). Adamu yace: “Ranar 10 ga watan Agusta, 2019, naje masallacin da yake karatu na Asshabulkhahfi, da kunne na, na ji yana batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a kan aurensa da Nana Safiyya (RA).”

An ruwaito cewa ana cikin sauraron shaidar ne Malam Abduljabbar ya ta shi yana mai cewa kamata ya yi a yanke mai hukuncin kisa. A cewar Shehin Malamin da ace ana zarginsa da cin mutuncin Manzon Allah (SAW) to gara a kashe shi kowa ya huta.

Ya kuma kara da cewa tun a baya ya nemi lauyoyinsa su ba shi dama ya nuna inda maganganun da yake faɗa suke a cikin litattafan Hadithi amma suka ƙi.

Ana cikin hakane sai lauyansa, Barista Umar Muhammad ya katse shi da cewa Malamin ya ɗauka kamar a kasuwa yake, inda zai iya faɗin abinda ransa ya so. Ya kara da cewa yasan cewa wannan shari’ar tana da hatsari sosai amma ya amsa, sai ga shi ba abinda malamin zai saka masa da shi sai zargi.

Alkali ya ɗage sauraron ƙara Da rikicin ya nemi yin ƙamari ne, Alkali Yola ya baiwa Shehin Malamin tare da lauyan nasa hakuri, sannan ya umarci Abduljabbar ya daina magana sai an nemi ya yi domin nan a kotu yake. Daga nan sai mai shari’a ya ɗage zaman har dai 28 ga watan Oktoba, za’a dawo domin cigaba da sauraron sheda ta biyu.

Labarai Makamanta