Kano: Abdul-Jabbar Ya Maka Ganduje Kotu

Sanannen Malamin nan mazaunin Kano da gwamnatin Jihar Kano ta haramtawa wa’azi Abdul-Jabbar Nasiru Kabara ya maka gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Ganduje Kotu a kan tsaresa da tayi ba bisa ka’ida ba.

Gwamnatin Kano ta hana Sheikh Abdul-Jabbar Nasiru Kabara wa’azi a ranar 4 ga watan Fabrairun 2021 a kan zarginsa da wa’azi da zai iya tada zaune tsaye, da haifar da ruɗani a jihar.

A ranar 7 ga watan Fabrairu na shekarar 2021 gwamnatin jihar ta amince da mukabala tsakanin Sheikh Abdul-Jabbar Kabara da sauran malaman addini a jihar ta Kano.

A wata takarda da aka mika gaban babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Laraba, Kabara ya ce abinda gwamnatin jihar Kano tayi masa yayi karantsaye ga hakkinsa na dan Adam da kuma addini.

Abdul-Jabbar Kabara na bukatar kotun ta umarci gwamnatin jihar, kwamishinan ‘yan sandan Kano da sauran jami’an tsaro da su gujewa musgunawa, hantara da duk wata takura da suke masa.

A yayin zantawa da manema labarai bayan shigar da karar, Shuaib Kabir, lauya mai wakiltar Kabara ya zargi gwamnatin jihar da yankarwa wanda yake karewa hukunci ba tare da sauraroronsa ba.

“Cigaba da tsare shi tare da mamaye gidansa da jami’an gwamnatin jihar suka yi yayi karantsaye ga hakkinssa na dan Adam,” lauyan yace.

Labarai Makamanta