Kanjamau: Najeriya Na Sahun Gaba Akan Sauran Kasashen Duniya

Har yanzu Nijeriya ita ce kan gaba a jerin kasashen da suka fi yawan mutanen da suke fama da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIB AIDS inda ta kasance kasa ta biyu a duniya. Tun lokacin da aka gano mutum

na farko wanda yake dauke da cutar a Nijeriya a shekarar 1986, ba za a iya cewa an samu wata gagarumar nasarar yaki da ita cutar ba. Bictor Omosehin, Shugaban kungiyar wadanda suka kamu da cutar HIB ta Nijeriya wato NEPHWAN, shi ya jagoranci taron tunawa da wadanda cutar ta hallaka inda kuma ya bayyana

yadda cutar ke ci gaba da yaduwa duk da kamfen na yaki da ita da ake yi inda Nijeriya ke bayan Afirka Ta Kudu a yawan mutane masu fama da cutar. Dogaro da tallafi daga kasashen waje na babban al’amarin da ya ke ta’azzara al’amuran, wanda ya ke ganin sai duk kungiyoyi da daidaikun mutane sun shiga kamfen sosai.

Ya ce, da a ce an mayar da hankali sosai wajen yaki da cutar kamar yadda aka yaki cutar Ebola, da tuni an cimma gagarumar nasara. Omoshehin ya cigaba da cewar, abin damuwa shine yadda cutar ke yaduwa a tsakanin ‘yan luwadi da basu fitowa fili su nemi magani, don tsoron hukuncin daurin shekaru 14.

Related posts