Kangin Talauci: Rungumar Sana’ar Noma Ne Mafita Ga ‘Yan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi yarda da iƙirarin cewa gwamnatin sa ba ta taɓuka komai a fannin Inganta tattalin arzikin ƙasa ba.

Ya bayar da amsar cewa mafitar ƙasar nan daga ƙalubalen tattalin arziki da kuɓuta daga talauci shi ne a koma gona a rungumi noma.

Haka ya faɗa a tattaunawar da Gidan Talabijin na Channels ya yi da shi, wadda aka nuna a ranar Laraba da dare.

A cikin tattaunawar sa da Seun Okinbaloye da Maupe Ogun-Yusuf, Buhari bai yarda da wasu alƙaluman ƙididdigar da matambayan biyu su ka bijiro masa da su ba, waɗanda su ka nuna masa cewa tattalin arzikin Najeriya tafiyar-kura ya ke yi tun bayan da Buhari ya hau mulki cikin 2015.

Cikin tattaunawar, an baje wa Buhari tantagaryar ƙididdiga da jadawalin tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tattalin arziki tsakanin 2015 zuwa 2021.

Labarai Makamanta