Kamfanin Simintin Dangote Ya Tafka Mummunan Asara

Rahotanni daga masana’antar sarrafa Siminti ta kamfanin Dangote na bayyana cewar masu hannun jari a kamfanin Simintin Dangote sun yi asara a cikin wannan makon yayinda arzikinsa ya samu nuksani cikin kwanaki hudu.

Masu hannun jari sun yi asarar N200 billion tsakanin Litinin da Alhamis. Wannan ya faru ne saboda tayin wawan da yan kasuwa ke yiwa hannun jarin kamfanin.

Haka ya sa arzikin kamfanin ya sauko N3.5 trillion a ranar Alhamis, daga N3.7 trillion a ranar farkon makon.

Hakan yana nufin an yi asarar akalla naira bilyan 200. Tun ranar Talata masu sanya sannun jari suka fara rage tayin da suke yiwa hannun jarin Dangote.

Labarai Makamanta