Kamfanin Jiragen Emirates Ya Sake Dakatar Da Zirga-Zirga A Najeriya

Kamfanin sufurin jirgin sama na Emirates mallakar Daular Larabawa wato United Arab Emirate (UAE) ya ce zai sake dakatar da zirga-zirga zuwa Najeriya daga ranar 13 ga Disamba.

Matakin kamfanin na zuwa ne bayan hukumar kula da sufurin jirgi ta Najeriya NCAA ta taƙaita wa kamfanin shiga Najeriya ta Abuja da Legas.

NCAA ta zargi hukumomin Daular Larabawa (UAE) da ƙin bai wa Air Peace, kamfanin Najeriya ɗaya tilo da ke shiga UAE, damar shiga birnin Dubai ta Sharjah.

Labarai Makamanta