Kamfanin Ɗangote Zai Kawo Ƙarshen Tsadar Abinci – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce an kawo karshen aikin kamfanin takin zamanin da mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya ke ginawa a jihar Legas.

Ministan harkar gona da cigaban karkara, Alhaji Muhammad Sabo Nanono, ya kai ziyara domin zagayawa ya ga wannan kamfani na Alhaji Aliko Dangote.

Jaridar Vanguard ta ce ministan ya kai wannan ziyara ne a karshen makon jiya, inda ya yabawa ‘dan kasuwar, ya ce kamfaninsa zai taimakawa harkar noma da samun saukin farashin kayan abinci.

Mai girma ministan ya yabawa Aliko Dangote da ya sa kudinsa wajen harkar takin zamani, wanda hakan zai sa farashin buhun taki ya rage kudi a Najeriya.

“Gwamnatin tarayya ta na son ganin ‘yan Najeriya su na da abin da za su ci. Za mu iya cin ma wannan buri ne kawai idan mu na da isasshen taki a kasa.”

Muhammad Sabo Nanono ya kara da cewa: “Ina matukar alfahari da abin da Aliko Dangote ya ke yi a kasar nan. Babu wanda ya ke yin irin rabin abin da ya ke yi.”

“Karfin takin Dangote ya isa ya canza yadda ake amfani da taki a kasar nan. Za mu dafa masa, mu kuma bada gudumuwa ga kokarin da ya ke yi.” Inji Nanono.

“Babu shakka takin Dangote zai taimakawa mutane da gwamnati.” Mai girma ministan ya ce kananan ‘yan kasuwa za su amfana da takin na Dangote.

Wani darekta na kamfanin Dangote, Devakumar Edwin, ya ce su na da dakin bincike inda ake auna karfin takin zamanin tare da duba kyawun kasar noma.

Devakumar Edwin, yace da kamfanin zamanin na Dangote, Najeriya za ta samu isasshen taki, har a rika fita da buhuna zuwa sauran kasashen Nahiyar Afrika.

Labarai Makamanta