Rahoton dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai yiwuwa jihohi 33 a Najeriya ba za su iya biyan albashi ba, saboda shirin gwamnatin tarayya na yanke kason kananan hukumomi domin fara yanke kudin da take biya na bashin dala miliyan 418 kwatankwacin naira miliyan 172 na kwararru kan kungiyar masu bayar da bashi ta kungiyar Paris Cub.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a rahotonta kan matsayin jihohi (‘State of States 2019′), BudgIT, wadda kungiya ce da ke sa ido kan harkokin kudi na gwamnati ta ce gwamnatocin jihohi uku ne kawai – Lagos da Rivers da Akwa Ibom, ne kawai za su iya biyan albashi da sauran harkokinsu na yau da kullum ba tare da samon kason gwamnatin tarayya ba.
Kungiyar gwamnonin Najeriya da sauran al’ummar kasar na matsa lamba domin daina biyan wadannan kudade da ake gani ba na gaskiya ba ne ga kwararrun.
Sai dai kuma a wani abu da ke bayar da mamaki, kasa da wata daya bayan da Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayar da umarni, ma’aikatar kudi da kasafi da kuma tsare-tsare ta fara zaftare kason kudaden da ake bai wa jihohi na kananan hukumomi domin biyan bashin.
Babban sakatare na ma’aikatar ya gaya wa taron kwamitin rabon kudade na tarayya a ranar JUma’a cewa, ma’aikatar ta fara yanke kudaden domin biyan bashin.
Wannan bayani ya harzuka jihohin, suka ki yarda da rabon watan Oktoba da ake ciki, har sai gwamnati ta dakatar da wannan yanka.
You must log in to post a comment.