Kalaman Momo Abin Allah Wadai Ne – Assalafiy

Na saurari hiran da Freedom Rediyo Kano tayi da ‘dan Hausa film Aminu Sheriff Momo, yana cewa Zakka da Musulmai ke fitarwa ya kamata ana ware Zakkan domin shirya fina finai..

Bai tsaya anan ba, Momo yace da a fitar da kudi a gina Masallatai da Islamiyyu yafi a fitar da kudin a gabatar da shirin film domin fadakarwa ne da gyara tarbiyya suke yi a film din, har yana hakikancewa

Jama’ar Musulmi ku ji zance banza fa, wato lalacewar wannan ‘dan nanaye da bayyana tsantsan duhun jahilcinsa har ya kai ga cewa shirin Film ya fi Masallaci dakin Allah daraja da kuma Islamiyyah inda ake koyar da Qur’ani da Hadisi?

Kullun suna cewa tarbiyya suke koyarwa a shirin film, amma me yasa ake samun ‘yan luwadi da madigo da karuwai a cikin su?
Me yasa ake samun wadanda ake yada bidiyonsu na tsiraici suna lalata?
Me yasa matan Hausa film suke bayyana babu hijabi tudun nonuwa da mazaunansu yana bayyana don jawo hankalin mazinata?

A gaskiya wadannan ba masu koyar da tarbiyya bane, muna kallon wadannan mutane ne a matsayin gurbatattun cikin mu marassa albarka karnukan farautar yahudawan duniya da akayi hayansu domin su batar da Musulmin kasar Hausa

Tsakani da Allah a cikin masu harkan film ba za’a rasa mutanen kwarai ba, amma kashi 99 cikin 100 dinsu ba mutanen kirki bane, babu irin tsiya da iskanci da basa yadawa a shirin film, Masallaci da Islamiyyah ba gurin yada tsiya bane, kuma ba gurin zuwan mutanen banza bane, sun fi karfin a kwatantasu da duk wani abu mai daraja anan duniya balle shirin film dangin yahudu

Muna Allah wadai da kalaman Momo, ya munana zance akan dakin Allah da inda ake karantar da addinin Allah, yayi magana kamar ya sha kwaya ko kayan maye ya bugu, tir da kalamansa akan addinin mu

Allah wadaran naka ya lalace!

Daga Datti Assalafiy

Labarai Makamanta