Kalaman Gumi Na Iya Haifar Da Basasa A Najeriya – Kayode

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya caccaki fitaccen malamin addini, Sheikh Dr Ahamd Gumi a kan tsokacinsa, inda yace a ninke yake a cikin duhu.

Fani-Kayode yayi martani ne a kan tsokacin Gumi inda yace in har za a iya yafewa masu shirya juyin mulki, me zai sa ba za a iya yafewa ‘yan binidga ba?

Fani-Kayode yace “Ta yuwu mu yiwa Hitler, Pol Pot, Stalin, King Leopard 11 na Belgium, Osama Bin Ladin, Al Bagdadi, Abubakar Shekau da duk wani wanda ya kashe mutane da yawa afuwa bayan mutuwarsu saboda tarihin da suka kafa a duniya.

“A farko ya bukaci ‘yan ta’addan da su mayar da hankali wurin harar sojoji kiristoci, daga baya yace satar yaran makaranta karamin laifi ne, yanzu kuma ya sauya salo.

“Ko dai Sheikh Ahmad Gumi ya rasa hankalinsa ne. Ko yana bukatar tallafin gaggawa na likitoci. Ko kuma ya zama mai magana da yawun ‘yan ta’addan da ke yankan rago, azabtarwa, fyade da garkuwa da mutane a kasar nan?”

Fani-Kayode yace ya sakankance Gumi baya cikin hayyacinsa kuma akwai wani abu da yake ba daidai ba da malamin.
“Kasar nan a halin yanzu tana dab da shiga cikin rikici. Kada Gumi ya hankada mu cikin rikici da tsokacinsa masu bada takaici da rashin ma’ana,”

Labarai Makamanta