Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad SAW.
An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same shi da dukkan laifi huɗu da ake tuhumar sa da su.
Mai Shari’a Sarki Yola ya ce malamin yana da kwana 30 don ɗaukaka ƙara idan bai gamsu da hukuncin ba.
Cikin iƙirarin da Abduljabbar ya yi a wa’azizzikan da ya sha gabatarwa, wadda kuma ake tuhumar sa a kanta, har da maganar cewa Annabi Muhammadu ya yi ƙwacen mata mai suna Safiyya daga wani sahabinsa.
Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce malamin “ya gaza kare wannan da’awa ko iƙirari da ya yi da karɓaɓɓun hujjoji”.
Ƙari a kan hukuncin kisa da kotun ta yanke, ta kuma ba da umarnin ƙwace dukkan litattafan da Sheikh Abduljabbar ya gabatar don kare kan sa da su.
Kotun ta ba da umarnin a miƙa litattafan ga Babban Ɗakin Karatu na Jihar Kano, sannan Kotun ta haramta saka karatun malamin a dukkan kafofin yaɗa labarai na jihar, tare da bai wa gwamnati shawarar ta ɗauki “duk matakin da ya dace” kan wadda ta saɓa umarnin.
You must log in to post a comment.