Kafatanin Gwamnonin Najeriya Za Su Yi Taron Gaggawa A Abuja

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban Daraktan kungiyar gwamnoninin Najeriya NGF
Asishana Okauru ya fidda sanarwar ganawar gaggawa na duka gwamnonin Najeriya 36 a Abuja

Wannan shine karon farko da za a yi taro ba ta yanar gizo ba.

Kamar yadda sanarwar ta ce, za a yi taron a Hedikwatar NGF ɗin ranar Laraba 19 ga wata.

” Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi na gayyatar duka gwamnonin ƙasarnan domin yin ganawa ta musamman don tattauna wasu muhimman batutuwa da suka taso.

Kakakin kungiyar, Abdulrazaque Bello-Barkindo ya ce tuni har an aika wa gwamnonin da takardar gayyatar.

” Za a fara ganawar tun daga karfe 8 na safe ranar Laraba sannan kuma bayan haka gwamnonin za su amsa tambayoyi daga manema labarai bayan haka.

Labarai Makamanta