Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Daniel Bwala wanda yana cikin kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku-Okowa ya ce mai gidansa ya fi kowa damar lashe zaben 2023.
A ranar Juma’ar nan, 6 ga watan Junairu 2023, Vanguard ta yi rahoton Daniel Bwala yana cewa akwai wasu Gwamnoni da Sanatocin APC da ke tare da su.
Bwala ya ce a wasu jihohin Arewacin Najeriya, akwai gwamnonin jihohi da ‘yan majalisar dattawa da aka zaba a APC da su na goyon Atiku Abubakar.
Mai magana da yawun bakin kwamitin takaran yake cewa wadannan ‘yan siyasa su na yi wa ‘dan takaran jam’iyyar PDP aiki ba tare da sun fito karara ba.
Wannan magana ta fito daga bakin Bwala ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin Arise a game da zaben 2023 kan mubaya’ar Olusegun Obasanjo.
“Gwamnonin Arewa 11, sannan ina tunanin da Sanatoci 35 zuwa 37 su na yi wa Atiki aiki a boye. Idan kun lura a wajen yakin neman zaben shugaban kasarsu, idan suka ce ‘Najeriya’, mutane za su amsa masu ne da cewa ‘Sai Atiku Abubakar!’. Shiyasa a taron karshe da suka yi a Kano a ranar Laraba, suka daina cewa ‘Najeriya’, domin sun san taron mutanen za su amsa ne da kiran Atiku.
You must log in to post a comment.