Kaduna Za Ta Tsayu Da Kafafunta Ba Tare Da Jiran Gwamnatin Tarayya Ba – El Rufa’i

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Nasiru Ahmad El Rufa’i tace ta na kokarin ganin ta samu duk kudin da ta ke bukata a kasafin shekara shekara daga abin da take samu a cikin gida.

Kwamishinan kasafi da tsare-tsare na Jihar Kaduna Alhaji Sani Dattijo ya bayyana hakan lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dokokin jihar Kaduna a cikin makon nan.

Kwamishinan yace idan aka cigaba da tafiya a haka, nan da wasu shekaru, duk abin da zai zo cikin asusun gwamnatin Kaduna bayan IGR zai zama nafila.

Salon shugabancin gwamnan na Jihar Kaduna ya zamo wani abu ba sa bamban ga al’ummar jihar, inda wasu ke yabo yayin da wasu ke suka.

Labarai Makamanta