Kaduna: ‘Yan Sanda Sun Hallaka Kwamandojin ‘Yan Bindiga Biyu

Labarin dake shigo mana yanzu daga Jihar Kaduna na bayyana cewar rundunar ‘Yan sandan Jihar sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga biyu da suka addabi yankin Ƙaramar Hukumar Giwa yayin wata arangama.

Dakarun rundunar 47 Zariya ne suka gamu da ‘yan fashin yayin da suke kan aikin sintiri a kusa da ƙauyen Riheyi na garin Fatika ranar Litinin da dare, in ji kakakin rundunar a Kaduna Mohammed Jalige

Da yake magana da Channels TV, Mista Jalige ya ce nan take suka fara fafatawa, inda jami’ansu suka yi nasarar kashe biyu daga cikinsu.

Ya ƙara da cewa ‘yan sanda sun ƙwace bindiagar AK-47 da kuma harsasai daga hannun ‘yan fashin.

A ranar Litinin ɗin da dare wasu ‘yan fashi suka tare babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya, inda rahotanni suka ce an kashe mutum ɗaya tare da sace wasu da dama.

Labarai Makamanta