Kaduna: ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Matafiya Sun Nemi Miliyan 200

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘Yan bindiga sun shaida wa iyalan ɗan sandan da suka sace su tattara musu miliyan N200m domin a sako shi saboda zasu bar wurin da babu sabis.

An ruwaito cewa Dan sandan mai suna Dambo Hosea, na ɗaya daga cikin matafiyan da aka sace ranar Lahadi, a kan hanyar Kaduna-Abuja. Shine jami’in dan sandan dake tare da tsohon ɗan takarar gwamnan Zamfara, wanda ƴan bindiga suka kashe yayin harin.

Tsagerun yan bindigan sun nemi iyalai su tattara musu zunzurutun kudi miliyan N200m domin sako shi cikin gaggawa kafin lokaci ya ƙure.

A kiran da suka wa iyalan ɗan sandan ta wayar salula, ‘yan bindigan sun bayyana cewa zasu bar wurin da ake samun sabis, don haka a biya fansa cikin lokaci. ‘Yan bindigan sun fusata yayin da iyalan mutumin suka roki zasu biya miliyan N2m, maharan sun fusata kuma suka ba su awanni 6 kacal su kawo miliyan N200m.

Wakilin mu ya saurari yadda ta kaya a hirar iyalan ɗan sandan da kuma masu garkuwan. Lokacin da aka roki za’a basu N2m, sai suka ce: “Bai kamata kuce haka ba bayan mun sace babban mutun kamar wannan, kuna faɗin abinda ba zai yuwu bane.

Kun ci sa’a abokan aiki na ba su ji ba.” “Lamarin zai girmama idan kuka ƙi biyan bukatar mu, idan kuka sake faɗin miliyan biyu, to ko dai mu harbe shi ko kuma mu yanka shi.”

Yayin da suka bashi damar yin magana, Hosea ya roki iyalansa su taimaka su biya kudin akan kari domin inda suke ba shi da kyau. “Mun yi doguwar tafiya kafin mu samu sabis mu kira ku, kuje wurin abokanaina idan ba zaku iya haɗa kudin ba, ku ci bashi idan na dawo zan biya.”

Da aka nemi wayar salulan kakakin yan sandan jihar Kaduna, Muhammed Jalige, ba’a same shi ba bare a ji ta bakin hukumar yan sanda.

Labarai Makamanta