Kaduna: ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Ɗaliban Jami’a Sun Bukaci Kudin Fansa

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘yan Bindigar da suka sace dalibai a wata jami’a mai zaman kanta a Kaduna mai suna Greenfield sun nemi kuɗin fansa har Naira Miliyan 800, Daya daga cikin iyalan daliban Jami’ar Greenfield da ke Kaduna ya ce ‘yan bindigan sun bukaci a biya Naira miliyan 800 matsayin kudin fansa kafin su sako daliban 23.

“Ana tattaunawa, masu garkuwar sun tuntubi wasu iyalan daliban suna neman a biya Naira miliyan 800,” a cewar, Georgina Stephen, yar uwan daya daga cikin daliban da aka ace.

A cewar Georgina, daliban 23 da aka sace sun kunshi mata 14 da kuma maza 6 da kuma ma’aikatan jami’ar.

Ta ce masu garkuwa da mutanen suna azabtar da daliban inda suka ce idan ba a biyan kudin ba, za su halaka dukkan daliban da suka sace.

Labarai Makamanta