Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sako Wadanda Suka Sace A Majami’a

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa sama da mutum 60 waɗanda aka sace daga cocin Emmanuel Baptist Church, da ke Kakau Daji sun koma ga iyalansu.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ne ya tabbatar wa BBC da hakan inda ya ce har da wasu mutane da aka yi garkuwa da su a hanyar Kachia zuwa Kaduna na daga cikin waɗanda suka samu ƴancinsu.

Ya bayyana cewa tun da farko sojoji ne suka tuntuɓi gwamnatin jihar Kaduna kan cewa akwai wasu mutane da dama waɗanda aka yi garkuwa da su da ke hannunsu, inda daga baya gwamnatin Kaduna ta karɓe su kuma ta miƙa su ga iyalansu da kuma shugabannin cocin.

Kwamishinan ya ce ba shi da tabbacin ko an biya kuɗin fansa kafin karɓo su ko kuma ƙwato su aka yi da ƙarfi.

Mambobin cocin dai sun shafe sama da wata guda a hannun masu garkuwa da mutane.

Labarai Makamanta