Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Saki Bidiyon Daliban Da Suka Sace

‘Yan bindigan da suka sace daliban makarantar koyar da dabarun noma da gandun daji dake Afaka Mando a jihar Kaduna sun bukaci N500m daga wajen gwamnatin jihar domin fansan dalibai 39 – Mata 23 da Maza 16.

Rahotonni sun bayyana cewa akalla iyayen uku cikin daliban sun tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun tuntubesu kuma sun bukaci N500m kafin su sakesu.Hakazalika ya bindigan sun sakin bidiyoyi uku na daliban da suka sace cikin daji.

Har yanzu gwamnatin jihar Kaduna ba tayi jawabi kan bidiyoyin ba kuma kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya ki amsa wayansa yayinda ake tuntubesa.

Amma, gwamnan Nasir El-Rufa’i a hirar da yayi a tashar Channels ya ce bai zai yi sulhu da ‘yan bindigan ba kuma ba zai biya kudin fansa ba.

‘Yan bindigan sun yi amfani da shafukan Facebook na daliban wajen sakin bidiyon ga jama’a.

A cikin bidiyon, ana iya ganin yadda ‘yan Bindigar suka zagayesu sanye da kayan Sojoji suna dukansu da fatar dorina.

A cikin bidiyon da aka saki misalin karfe 12:00 na ranar Asabar ta manhajar Facebook na Tasha Sandra, ana iya ganin daliban cikin daji tare da yan bindigan suna dukansu.

Tasha Sandra tace: “Wannan ba bidiyon bogi bane. Ku taimakemu ku biya kudin da suke bukata kuma kada kuyi kokarin turo Sojoji ceto mu saboda zasu kashemu.”

“Ina kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jiha su kawo kudin fansa N500 million. Ga lamba daya tilo da za’a iya samunsu 09023404650.” Daya daga cikin daliban yace:

“Suna na Abubakar Yakubu. Dalibin kwalejin gwamnatin tarayya na ilmin gandun daji Kaduna. Ina kira ga gwamnan jihar Kaduna, gwamnatin jihar Kaduna da gwamnatin tarayya.”

Labarai Makamanta