Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sace ‘Yan Mata Masu Rubuta WAEC

LYan Ta’adda Sun Kwashe ‘Yan Matan Makarantar Prince Academy Dake Kaduna

Yanzu haka ‘yan ta’adda sun kwashe ‘yan matan makarantar Prince Academy dake karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna a daidai lokacin da suke rubuta jarabawar karshe (WAEC).

Su dai wadannan ‘yan ta’adda sun je garin Chikun ne akan babura sama da dari, inda suka ratsa garuruwa daban-daban kafin su isa garin Chikun.

Sha’anin tsaro na cigaba da samu tarnaki a jihar tun bayan da ‘yan Bindiga suka dawo da harkokin su a jihar Kaduna, lamarin da ya jefa jama’ar jihar cikin zaman ɗar ɗar.

A cikin makon nan da muke ciki Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’adu Abubakar ya ziyarci Gwamna El Rufa’i inda suka tattauna hanyoyin da za’a bi wajen magance matsalar tsaro da ta addabi jihar.

Labarai Makamanta