Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sace Hakimi Da Wasu Manyan Birnin Gwari

Lamarin ya faru a ɗazu da misalin karfe 12 na rana wasu yan bindiga dauke da muggan makamai suka diro garin na Birnin Gwari inda sukayi garkuwa da Alhaji Yusuf Yahaya Mai Dubu (sarkin kudun birnin gwari) da sakataren ilimi na karamar hukumar birnin gwari

Kamar yadda Muryar Yanci ta samu ruhoton yanzu daga birnin gwari, daya daga cikin wanda akayi garkuwan dasu wanda ake kira Alhaji Magaji Umar jagaban birnin gwari ya arce amman haryanzu shima ba a ganshi ba, saidai wata majiyar tace a yanzu haka yana hannun jami’an tsaro na yan sanda dake buruku wani kauye dake hanyar kaduna zuwa birnin gwari. Sarkin kudun birnin gwari yusuf yahaya Mai Dubu ya kasance hakimi a masarautar na karamar hukumar birnin gwari ,

Related posts