Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar Gwamna Uba Sani

Rahoton dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kaddamar da hari akan ayarin motocin ɗan takarar gwamna na APC Uba Sani inda suka yi awon gaba da wasu jiga-jigan jam’iyyar ta APC a babban titin Kaduna-Kachia dake kudancin Jihar.

An ruwaito cewa harin ya auku ne a Tashar Icce, kusa da garin Kujama dake karamar hukumar Kajuru. Tawagar jiga-jigan na hanyarsu ta komawa gida ne bayan ganawa da jagororin Kiristoci a kudancin Kaduna ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewar daya daga cikin yan siyasan da ya tsallake rijiya da baya yace kimanin motoci biyar yan bindigan ɗauke da muggan makamai suka budewa wuta.

Ya ce an yi awon gaba da mutum biyu yayinda wasu mutum uku suka jikkata. An tattaro cewa dan takaran gwamnan jihar Sanata Uba Sani, bai cikin motar saboda ya tafi Abuja daga Kafanchan.

An tuntuban Kakakin Rundunar yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalinge. Ya bayyana cewa zai nemi karin bayani kan lamarin kuma zai tuntubemu.

Labarai Makamanta