Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Ci Zarafin Mu A Zaman Mu A Daji -Ɗalibai Mata

Bayan sakin ɗaliban nan 27 na kwalejin nazarin harkar gandun daji ta Kaduna da ke Najeriya, wadanda suka kwashe kwana 50 a hannun ‘yan bindigar da suka sace su, BBC Hausa ta zanta da ɗaya daga cikinsu, inda ta bayyana irin uƙubar da suka sha.

Dalibar, wadda muka sakaya sunanta saboda dalilan tsaro, ta ce tsawon kwana 50 din da suka kwashe a hannun mutanen suna kwana ne a ƙasa – akan yanko ganyen bishiya ne sannan a bukaci su kwanta a kai.

Ta ce hatta abinci babu wani na kirki, miyar kuka ce ba wani sinadarin ɗanɗano, haka da ɗaɗi ba ɗaɗi suke daure su ci, a ci kar a mutu.

Dalibar ta kara da cewa sun sha fama da cin fuska da raini iri-iri a wajen ‘yan bindigar har zuwa yanzu da Allah Ya kawo silar kubuta daga hannunsu.

”Mu 37 ne aka dauka, ciki har da maza 15, sun zo ne a kan babura muna bacci a makaranta suka zo suka tashe mu, a kafa muka rika tafiya har muka zo wajen da suka ajiye baburansu, sai muka hau muka ci gaba da tafiya” in ji ɗalibar.

Ta ce haka suka rika kwana cikin sauro, ruwa sai an je rafi ake debowa, “shi ma mazan da aka sace mu da su ne suke zuwa can su debo domin mu yi amfani da shi.”

Ta kara da cewa ‘yan bindigar ne ke yi musu jike-jike irin na gargajiya da sirace idan wasu daga cikinsu na fama da rashin lafiya.

Dalibar ta ce ‘yan bindigar sun yi ta zaginsu suna cewa za su kashe su idan ba a bayar da kudin fansa ba.

A cewarta yanzu da ta koma wajen iyayenta, tana cikin farin ciki, domin babu inda ya fi gida kwanciyar hankali.

Kafafen watsa labarai a Najeriya dai sun rawaito cewa an kubutar da daliban ne sakamakon sasancin da fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya jagoranta, tare da shawarar tsohon shugaban Najeriya Oluseagun Obasanjo.

Matsalar tsaro da satar mutane musamman dalibai a makarantu domin neman kudin fansa dai na ci gaba da karuwa a Najeriya, ko da yake mahukunta kan ce suna iya bakin kokarinsu domin kawo karshen matsalar.

Labarai Makamanta