Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Bukaci Fansar Miliyan 200 Na Sojan Da Suka Sace

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Yan bindigan da suka kai hari makarantar horar da Sojojin Najeriya NDA dake garin Afaka a jihar Kaduna kuma sukayi awon gaba da jami’in Soja sun kira gidan Soja inda suka bukaci kuɗin fansa.

Sojan da akayi awon gaba da shi sunansa, Manjo Dantong. A cewar FIJ, yan bindigan sun kira NDA domin tattauna maganar kudin fansa kafin su sake shi. Sun bukaci a basu kudi N200m idan har ana son Manjon ya dawo da ransa.

Wata majiyar FIJ ta bayyana cewa: “Ko mutum daya sun kasa kashewa. Sun duba ko ina cikin daji amma basu gansu ba. Sun gudu kan baburansu.”

“Sun kira kuma sun bukaci kudin fansa N200m don sake Manjon. Wannan harin abin takaici ne. Sun shigo, sun mamaye mu kuma sun tafi.” “Ko jirgi mai saukar angulun da aka tura yawo cikin daji bai gansu ba.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply