Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Bindige Uba Da Ɗan Shi

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ƙauyen Baka da ke Ƙaramar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, inda suka kashe uba da ɗansa.

‘Yan fashin waɗanda suka yi wa garin tsinke da farar safiyar yau Asabar, sun je ne domin yin garkuwa da wani manomi da ɗansa, a cewar Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan.

Sanarwar da kwamishinan ya wallafa a Facebook ta ce mutanen sun ƙi yarda ‘yan fashin su tafi da su, abin da ya sa suka harbe su nan take.

Sai dai sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wasu ‘yan fashi yayin wasu hare-hare ta sama ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa bayan an gan su tare da shanun da suka sata, a cewar Aruwan.

Matsalar kashe-kashe da ‘yan fashi ke yi a Jihar Kaduna ta zama ruwan dare, duk da cewa gwamnati da jami’an tsaro na cewa suna bakin ƙoƙarinsu.

A makon da ya wuce ma ‘yan fashin sun kashe mutum 23 a hare-haren da suka kai a ƙaramar hukuma uku cikin kwana ɗaya.

Mai bai wa Buhari shawara kan tsaro zai gana da gwamnonin arewa maso yamma
Mai bai wa Shugaban Najeriya Buhari shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), zai yi wata ganawa tare da gwamnonin yankin arewa maso yammacin ƙasar ranar Litinin.

Wata sanarwa da ofishin tsohon sojan ya fitar ta ce za a yi tattaunawar ce a Kaduna, wadda za ta mayar da hankali kan matsalolin ‘yan fashin daji da suka addabi yankin.

Da ma dai akwai rashin fahimta tsakanin gwamnonin yankin game da hanyoyin shawo kan matsalar, inda wasunsu ke cewa a yi sulhu tare da yi wa miyagun afuwa, wasu kuma ke cewa a yaƙe su.

A farkon makon nan ne Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya faɗa wa BBC cewa “idan gwamnatin tarayya ba ta ba mu sojoji na sama da na ƙasa ba, an shiga dazukan nan an kashe ‘yan ta’addan nan a lokaci ɗaya, to za mu ci gaba da zama cikin matsala”.

Ita kuwa gwamnatin Zamfara na ganin yin sulhu ne mafita, har ma kwamishinan tsaronta ya faɗa ta cikin shirin Ra’ayi Riga na BBC cewa “muna ganin alfanunsa kuma an samu sauƙi sosai”.

Kaduna na samun goyon bayan Jihar Neja a wannan batu, yayin da Zamfara da Katsina ke shafi ɗaya.

Shi ma Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya tofa albarkacin bakinsa, yana mai sukar El-Rufai game da amfani da ƙarfin soja kaɗai a kan ‘yan bindigar.

Labarai Makamanta