Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Bindige Direban Sarkin Birnin Gwari

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘yan bindiga a ranar Asabar sun hallaka daya daga cikin direbobin Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibrin Maigwari II a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

An ruwaito cewa bayan kashe direban mai suna Nasiru Sarkin Zango, ‘yan bindiga sun bankawa motar fada kirar Toyota Hilux wuta.

An tattaro cewa wannan hari ya auku ne misalin karfe 3 na ranar yayinda direban ke hanyarsa ta komawa Birnin-Gwari daga Kaduna bayan gyaran motar.

Rahoton ya kara da cewa majiyoyi daga cikin fada sun bayyana cewa Nasiru Sarkin Zango kadai ke cikin motan lokacin da aka kai harin.

Hakazalika ‘yan bindigan sun kai harin ne wajen dajin Unguwan Yako, daidai inda aka kaiwa ayarin motocin sarkin hari a watan Maris amma ba ya ciki lokaci.

Wata majiya ta bayyana cewa an tafi da gawar mamacin cikin garin Birnin Gwari don jana’iza Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da lamarin.

Wani mazaunin Birnin Gwari, Datti AbdulRauf ya bayyanawa mana cewa: “Gaskiyane har anyi janazarsa bayan magrib muka dawo daga rakiyarsa a maqabarta. Ya Allah duk Masu siyasantar da matsalar tsaron ya Allah kahadasu da mummunan ajali.”

Labarai Makamanta