Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Antaya Daji Da Tsala-Tsalan ‘Yan Mata

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar aƙalla mutum 18 ƴan bindiga suka sace tare da kashe mutum guda a Angwar Zalla Udawa a Ƙaramar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani jagora a wurin da lamarin ya faru inda ya ce cikin waɗanda aka sace har da matan aure da ƴan mata.

An bayyana cewa ƴan bindigan sun kai harin ne da misalin 12:30 na daren Asabar wayewar garin Lahadi a garin da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

BBC ta tuntuɓi mai magana da yawun ƴan sanda reshen jihar Kaduna Mohammed Jalige domin jin ƙarin bayani sai dai bai amsa kiranmu ba.

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ƴan bindiga suka addaba inda suke ci gaba da sace mutane domin karɓar kuɗin fansa da kashe su a wani lokacin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply