A kalla sama da ‘Ya’ yan Jam’iyyar PDP 12,870 wadanda suka hada da, tsofaffin Shugabanin Jam’iyyar PDP da mambobin Jam’iyyar, da kuma wasu saura mambobin da Shugabanin jam’iyyun adawa ne suka canja sheka zuwa Jam’iyyar APC a karamar hukumar Giwa.
Taron amsar dubban masu canja shekar ya gudana ne a Karkashin jagorancin Sanata Mai Wakiltar Al’ummar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, wanda kuma har ila yau, shi ne Dan takarar gwamna Jihar Kaduna a Karkashin inuwar jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani.
Taron wanda ya gudana a filin taro dake karamar hukumar Giwa.
A yayin da yake jawabi, Sanata Uba Sani, ya bayyana ma dubban wadanda suka dawo jam’iyyar APC cewa, za’a yi tafiya da kowa bisa adalci, amana da bin tsari dokoki irin na jam’iyyar
Sanata Uba Sani ya kara da bayya na cewa, a irin yadda ya ga taron dubban Shugabanin da mambobin jam’iyyar PDP wanda suka sauyawa sheka zuwa jam’iyyar APC, tabbas ya kara tabbatar da cewa, jam’iyyar PDP ta mutu murus a karamar hukumar Giwa.
A yayin da yake nasa jawabin a madadin wadanda suka canja shekar, jigo a jam’iyyar PDP, Honarabul Ahmed Sama’ila Yakawada, ya bayyana cewa, jin dadin irin dimbin ayyukan ci gaba da jam’iyyar APC ta gudanar a karamar hukumar Giwa da ma Jihar Kaduna baki daya, shi ne ya janyo ra’ayinsu suka yanke shawarar dawowa jam’iyyar APC mai adalci ga kowa.
Tun farko a nasa jawabin, Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kaduna, Air Commodore Emmanuel Jekada (rtd), ya yi kira ga Al’ummar karamar hukumar Giwa, da su zabi jam’iyyar APC tun daga sama har kasa.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada, da Dan takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya, Honarabul Muhammed Sani Dattijo, da Dan takarar Majalisar tarayya Birnin Gwari da Giwa, wanda kuma shi ne tsohon kakakin majalisar dokokin Jihar Kaduna, Honarabul Bashir Zubairu Ciroman Birnin Gwari, da kuma Shugabanin Kananan Hukumomi, Daraktan kamfen yakin naiman zaben Sanata Uba Sani, Farfesa Muhammad Sani Bello (Mainan Zazzau), daraktoci da mambobin kamfen, da kuma sauran dimbin ‘ya’yan jam’iyyar APC dake Jihar Kaduna.
You must log in to post a comment.