Kaduna: Sarkin Masarautar Gwari Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Allah ya yi wa Dr Danjuma Barde, sarki mai sanda mai daraja ta ɗaya a ƙaramar hukumar Chikun rasuwa.

Basaraken ya mutu ne a safiyar ranar Laraba Rahotanni sun ce ya mutu ne a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna bayan doguwar jinya.

Kungiyar cigaban Gwarawa ta GDA ta tabbatar da rasuwar sarkin, Peter Aboki, shugaban kungiyar cigaban Gbagyi, GDA, ya tabbatar da rasuwar basaraken a ranar Laraba.

Aboki ya ce: “Mun rasa basaraken mu, ya dade yana fama da rashin lafiya. Ya rasu a safiyar yau a asibitin sojoji na 44 na Kaduna.”

Labarai Makamanta