Zababben Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya amince da nadin Malam Muhammad Shehu Lawal a matsayin babban sakataren yaɗa labarai na gwamnatinsa.
A cikin wata sanarwar da zaɓaɓɓen Gwamnan ya fitar ya bayyana cewar nadin ya fara aiki ne tun daga ranar 23 ga watan Mayun da muke ciki.
Muhammad Shehu Lawal gogagge ne kuma Ƙwararre a bangaren aikin sa a tsawon shekaru 10 da ya yi yana ayyuka daban daban ta fuskar Siyasa taimakon al’umma da sauran muhimman al’amura.
Lawal wanda ake yi wa lakabi da Molash ya mallaki takardar shaidar karatu ta digirin digirgir a fannin siyasa a jami’ar Ahmadu Bello Zariya, sannan ya mallaki shaidar digiri bangaren daidaito da wanzar da zaman lafiya a jami’ar jihar Kaduna, sannan ya yi manya manyan kwasa kwasai a cikin gida da kasashen waje.
Muhammad Shehu Lawal ya riki muƙamin babban Mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Kaduna kan harkokin siyasa daga shekarar 2019-2023. Sannan ya taka muhimmiyar rawa ta fuskar yaɗa labarai da yaƙin neman zaɓen Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna da shiyyar Arewa maso yamma a yaƙin zaɓen Shugaban Kasa.
Zababben Gwamna Uba Sani ya bukaci wanda aka nadan da ya yi tukuru wajen inganta alaƙa da ‘yan Jaridu da ciyar da jihar Kaduna da jama’arta gaba.
You must log in to post a comment.