Kaduna: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Yi Nasarar Cafke Barayin Shanu

A ranar Larabar ne rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kaduna, ta yi nasarar kama a kalla mutane 79 da ake zargi ’yan ta’adda ne tare da kwato shanu 439.

Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Ali Janga ne ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai a garin Rijana dake karamar hukumar Kachia.

Ya ce, “Jami’an mu na SARS, AKU, IRT sun sami nasara sosai yayin da suka kamo wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban har su 79.”

Related posts