Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce gwamnatin jihar ta kashe N16 billion kan maganace matsalar tsaro cikin shekaru biyar da suka gabata.
Kamfanin dillancin labarai na Ć™asa ya ruwaito cewa El-Rufa’i ya bayyana hakan ne yayin ganawa da kwamitin sarakunan gargajiyan jihar ranar Talata.
Yawaitan rashin tsaro a jihar Kaduna ya zama abin damuwa ga gwamnati da mazaunan jihar.
A watan Yuli, akalla mutane 50 aka kashe a garuruwan kudancin Kaduna kadai.
Gwamnan ya ce an yi amfani da kudin ne wajen taimakawa jami’an tsaro wajen sayan kayan fasaha domin dakile matsalar tsaron jihar.
Ya ce da anyi amfani da kudin wajen ayyukan cigaba jihar “da mutane sun zabi zama lafiya”
El-Rufa’i ya ce daga cikin karerayin da ake yi kan wannan rikici na kudancin Kaduna shine maganar cewa ana kokarin kawar da wasu kabilu da kwace musu filaye.
A cewar El-Rufa’i, babu kwayar gaskiya ciki wannan ikirari.
“A matsayina na gwamna, na baiwa duk wani sarkin gargajiya dama dan Allah ya fadawa manema labarai wani shibirin filin kasarsa da aka kwace masa karfi da yaji ba bisa hakki ba kuma ina tabbatar muku cewa jam’ian tsaro za suje su kawar da su,”
“Amma abinda na sani – kuma ina samun bayanan hukumomin tsaro kulli yaumin, babu wani abu mai kama da haka da gwamnatin jihar ta sani.”
“Amma bamu san komai ba, kun fi mu sani saboda kun fi kusa da al’umma, saboda haka ku kawo rahoton duk inda yan bindigan ko wasu suka kori mutane.” Ya ce
El-Rufa’i ya ce gwamnatin za ta cigaba da taimakawa hukumomin tsaro wajen dawo da zaman lafiya yankunan da rikicin ya shafa.
Ya yi kira ga dukkan sarakunan gargajiya su taimaka wajen shawo kan mutane su zabi zama lafiya kuma su taimaka wajen watsi da karerayin da ake yi kan rikicin kabilun dake faruwa a wasu sassan jihar.
You must log in to post a comment.