Kaduna: Matasa Sun Kone Dillalin ‘Yan Bindiga Kurmus


Wasu matasa a yankin ƙaramar Hukumar Igabi a jihar Kaduna sun Lakadawa wani mutum Mai suna Abdullahi Mohammad Gobirawa Dukan da ya Zama ajalinsa, tare da kone gidan sa.

Fusatattun matasan sun aikata hakan ne sakamakon zargin mutumin da Zama Jakadan Yan bindiga wadanda suka addabi jihar.

Da yake Karin haske Kan lamarin Kwamishinan Kula da harkokin tsaro da alamuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya ce Matasan sun aikata hakan ne, bayan da zarginsu ya yi karfi duba da yadda aka samu wasu da aka Yi garkuwa su a yankin nasu.

Ya kuma tabbatar da cewa Matasan sun hallaka mutumin, bayan sun kone gidansa, Sai dai yace bayan da Gwamnan jihar Nasiru Elrufai ya samu rahoton yayi Allah wadai da yadda Matasan suka dauki doka a hannunsu.

Labarai Makamanta