Kaduna: Matan Aure Na Tura ‘Ya’yansu Mata Wajen ‘Yan Bindiga Neman Kudi – Kwamishina

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Hafsat Baba, kwamishinar Mata da kula da ayyukan jama’a ta jihar Kaduna ta bayyana cewa, yana da matukar muhimmanci a magance wasu matsaloli da suka dumfaro mata a jihar.

Ta bayyana cewa, akwai matan dake tura ‘ya’yansu mata ga ‘yan ta’adda su yi lalata dasu saboda kawai su samu kudin kashewa.

Da take magana kan ci gaban diya mace da kuma tsaronta a makaranta, kwamishinar ta ce, iyaye mata dake tura ‘ya’yansu aikace-aikace da tallace-tallace na taimakawa wajen kara yawan adadin yaran da ba sa zuwa makaranta.

Hakazalika, kwamishinar ta bayyana damuwa game da halayen wasu iyaye wajen tabbatar da tsaron ‘ya’yansu a kasar nan A cewarta: “Mun yi magana game da rashin tsaro amma har yanzu akwai abin zargi kadan.

Meye za a ce game da masu kai wa ‘yan bindiga bayanai? “Daga cikinmu suke, suna ba ‘yan bindiga bayanai saboda sun mai da hakan kasuwanci. Na ga mata na ba da ‘ya’yansu mata ga ‘yan bindiga, su kwanta da ‘yan bindiga domin kawai su sami kudi.

Labarai Makamanta