Kaduna: Mataimakin Shugaban ‘Yan Sanda Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Mataimakin Babban Sufeton ‘yan-sandan Najeriya da ke shugabantar sashe na 12 da ke Bauchi, Audu Madaki, ya tsira da ranshi amma ya samu raunuka daga harsashi a lokacin da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai wa motarsa hari a kusa da garin Kwoi da ke Jihar Kaduna.

An kai wannan hari ne ranar Talata a lokacin da AIG din yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Bauchi, tare da ma’aikatansa ba tare da motocin masu tsaronshi ba.

Wasu majiyoyin tsaro wadanda ba su yarda a bayyana sunayensu ba sun bayyana cewa maharan sun je ne a cikin mota kirar Sharon suka bude wa motarsa wuta.

Majiyoyin sun kara da cewa Mr. Madaki ya samu raunuka biyu na harsashi a kafarsa, shi kuwa mai tsaron lafiyarshi ya rasa ransa.

Daya daga cikin majiyoyin ya bayyana cewa AIG din ya yi kuskure da ya bi wannan hanya mai hadari ba tare da jerin motocin masu tsaronshi ba.

Labarai Makamanta